Jam’iyyar APC ta mayar da martani ga dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, Rabiu Kwankwaso, dangane da tayin da ya yi na kula da Atiku Abubakar idan har tsohon mataimakin shugaban kasar ya janye daga takarar shugaban kasa ta shekarar 2027.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar a matakin kasa, Felix Morka, ya nuna shakku kan yadda ‘yan adawa ke nuna kwarin gwiwar tattaunawa kan batun kujerar shugaban kasa kafin ‘yan Najeriya su zabi wanda zai hau kujerar a shekarar 2027.
A cewarsa, wannan lamari yana nuna abin da ya kira munafunci a cikin bangaren ‘yan adawa.
“Daga karshe, an yaye labulen… ga shi nan an tona asirin masu nuna kamannin tsarki a waje alhali a ciki suna cike da warin cin hanci da rashawa da kuma munafunci mai muni,” in ji Morka.
Morka ya kara da cewa jam’iyyar adawa na yin cinikin siyasa ne kan mukamin da ba ta lashe ba, kuma babu wani tabbacin za ta samu.
A tuna cewa Kwankwaso ya yi kira ga Atiku da ya janye kudirinsa na neman shugabancin kasa, ya kuma goyi bayan tikitin takarar Obi da Kwankwaso a zaben shekara mai zuwa.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya yi nuni da shekarun Atiku da yanayin lafiyarsa, inda ya kara da cewa za a kula da tsohon mataimakin shugaban kasar idan tikitin jam’iyyar adawar ya lashe zaben shugaban kasa.
