Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya sha alwashin yin wa’adi ɗaya na shekaru huɗu kacal idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Najeriya a 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawar jam’iyyar APM da al’umma a yankin Arewa maso Gabas, wanda aka gudanar a Yola, Jihar Adamawa.
Ya ce gwamnatinsa za ta kasance ta haɗin kan ƙasa, wadda za ta haɗa kowane ɓangare na Najeriya, tare da mayar da hankali kan gaskiya, gaskiya da riƙon amana a mulki.
Gwamnan ya kuma ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya bayyana tsarin da gwamnatin tarayya ke amfani da shi wajen ƙayyade farashin man fetur, yana mai cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake tsara farashin.
Makinde ya soki wasu manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da amfani da iskar gas ta (CNG), motocin lantarki da shirin musayar ɗanyen mai da naira, yana mai cewa ba su samar da sakamakon da ake tsammani ba.
Ya kuma tunatar da shugaban ƙasar alƙawarin da ya ɗauka na inganta wutar lantarki cikin shekaru huɗu, yana mai cewa zaɓen 2027 ya kamata ya kawo ƙarshen siyasar yaudara da rashin cika alƙawura.
A cewarsa, jam’iyyar APM za ta tsara manufofinta ne bayan sauraron ra’ayoyin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa shirinta na tafiyar da ƙasa ya dace da buƙatun ’yan Najeriya.
A nasa jawabin, jagoran jam’iyyar APM na ƙasa kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce jam’iyyar ta zama babbar ƙarfi a tsakanin jam’iyyun adawa, yana mai kira ga magoya bayanta da su mara mata baya.
Shi ma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar, Lawal Daura, ya ce Najeriya na buƙatar sauyi mai zurfi domin sauya alkiblar ƙasar da inganta rayuwar al’umma.
