’Yan bindigar da suka sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) a jihar Kogi sun buƙaci a biya Naira miliyan 20 kan kowane ɗaya domin sakin waɗanda ke hannunsu.
Rahotanni sun ce an sace jami’an NYSC ne yayin da suke dawowa daga sansanin horas da su na jihar Bayelsa zuwa Abuja, a kan hanyar Aloma-Egane da ke ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Rundunar ’yan sandan Kogi ta tabbatar da cewar an ceto wasu daga cikin waɗanda aka sace, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da sauran.
Iyalan wasu daga cikin waɗanda suka rage a hannun masu garkuwar sun ce an tuntube su tare da neman Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa ga kowane mutum.
