Gwamnatin Jihar Katsina ta karrama Kwamishinan Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane, Dr. Faisal Umar Kaita, da lambar yabo ta Best Performing Commissioner of the Year 2026.
An gabatar da lambar yabon ne yayin bikin cika shekaru 39 da kafuwar Jihar Katsina, wanda aka gudanar a Zauren Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari House, a Katsina.
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umaru Radda, shi ne ya gabatar da lambar yabon a madadin gwamnatin jihar.
An bayyana cewa an karrama Dr. Faisal Umar Kaita ne bisa jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan Ma’aikatar kasa da tsara Birane, inganta tsarin amfani da filaye, da kuma tallafa wa manufofin gwamnatin jihar na bunkasa birane da samar da ingantaccen tsarin kula da filaye.
Gwamnatin ta ce Ma’aikatar kasa da ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin filaye da tsara birane, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Jihar Katsina.
Bikin cika shekaru 39 da kafuwar Jihar Katsina ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin ma’aikatun gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Bikin ya kuma kasance wata dama ta duba irin ci gaban da jihar ta samu tun bayan kafuwarta a shekarar 1987, da kuma karrama wasu daga cikin jami’an da suka taka rawa wajen ci gaban jihar
