Masu sayen fetur a Najeriya na jiran saukin farashi bayan da Dangote Petroleum Refinery da wasu masu sayar da mai a depots suka rage farashin fetur a Legas da wasu manyan birane.
Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote ta rage farashin fetur a depot daga N1,350 zuwa N1,325 kan kowace lita, wato raguwar N25.
Haka kuma, wasu kamfanonin mai da suka hada da Ascon, Integrated, Pinnacle da Sahara sun rage farashinsu da kusan N24 kan kowace lita; farashinsu yanzu yana zagaye N1,326 zuwa N1,327.
MRS kuma ta rage farashinta da N20 zuwa N1,332, yayin da Wosbab ke sayarwa kan N1,330.�
Ana alakanta wannan saukar farashi da faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Idan masu gidajen mai suka cike tankokinsu da sabon kaya a farashi mai rahusa, ana sa ran farashin da masu ababen hawa da sauran jama’a ke biya zai iya sauka a hankali.
Sai dai rangwamen bai bayyana sosai ga masu saye a ko’ina ba tukuna.
Rahotanni sun ce a wasu wurare, ana ci gaba da sayar da fetur tsakanin N1,370 da N1,450 kan lita duk da saukar farashin depot.
Wannan na nuna cewa akwai tazara tsakanin farashin da dillalai ke saye da kuma farashin da masu amfani na karshe ke biya.
Ma’aikatar albarkatun man fetur ta ce farashin fetur a Najeriya ya fi sauki idan aka kwatanta da wasu kasashen Afirka da Amurka.
Amma ga yawancin ‘yan Najeriya, muhimmiyar tambaya ita ce: shin raguwar farashin depot za ta sa farashin sufuri da kayan abinci su sauka?
