Gwamnatin Tarayya ta sake bayyana cewa ba ta da shirin dawo da tallafin man fetur, duk da ci gaba da muhawara kan tsadar rayuwa da tasirin cire tallafin ga ’yan Najeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin lacca ta cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Akume ya ce cire tallafin man fetur na daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka tun shekarar 2023 domin sake daidaita tattalin arzikin ƙasar.
Ya ce matakin, tare da sauye-sauyen kasuwar canjin kuɗin waje da wasu gyare-gyaren haraji, sun kasance masu wahala, amma gwamnati ta yi imanin cewa sun zama dole domin dawo da daidaiton tattalin arziki.
Gwamnatin ta ce ba za ta koma tsarin tallafin da ta bayyana a matsayin tsohon tsari mai lalata tattalin arziki ba, inda ta jaddada cewa yanzu hankalinta ya koma kan tabbatar da cewa ci gaban tattalin arzikin ya haifar da ayyukan yi da ƙarin kuɗin shiga ga ’yan Najeriya.
A wani bangare, gwamnatin ta ce tana ƙara mayar da hankali kan amfani da CNG a matsayin madadin man fetur wajen rage kuɗin sufuri. Akume ya ce sama da motoci 120,000 aka sauya zuwa CNG, tare da cibiyoyin sauya motoci sama da 400 da tashoshin CNG kusan 90 a faɗin ƙasar.
Sai dai batun cire tallafin man fetur na ci gaba da kasancewa babban batu a tsakanin ’yan Najeriya, musamman saboda alaƙarsa da farashin sufuri da tsadar kayan masarufi.
A nasa jawabin ranar ’yancin kai, Shugaba Tinubu shi ma ya yi watsi da kiraye-kirayen komawa tsarin tallafin man fetur, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta koma kan abin da ta ɗauka a matsayin tsohon tsarin tallafi ba.
