Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 27, Sada Tambai bisa zargin kashe mahaifinsa mai shekaru 80, Adamu Tambai, a ƙauyen Mundadu da ke ƙaramar hukumar Bindawa.
A cewar ’yan sanda, lamarin ya faru ne ranar 21 ga Satumba 2026, bayan an samu rahoton cewa tsohon shugaban unguwar Mundadu yana kwance ba ya motsi a gaban gidansa.
An garzaya da shi asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa. Binciken farko ya kai ga kama ɗansa.
’Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya amsa yayin tambayoyi cewa ya bugi mahaifinsa da sanda, lamarin da ya haifar da raunukan da suka yi sanadin mutuwarsa.
An tura lamarin sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin ci gaba da bincike, sannan ’yan sanda suka ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
