Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce sama da ’yan Najeriya miliyan 140 na rayuwa cikin matsanancin talauci.
Obi ya bayyana hakan ne a cikin saƙon ranar ’yancin kan Najeriya na 1 ga Oktoba, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Ya ce bikin ranar ’yancin kai ya kamata ya zama lokacin yin nazari kan halin da ƙasar ke ciki, maimakon mayar da shi biki kawai.
A cewarsa, sama da yara miliyan 18 ne ba sa zuwa makaranta, yayin da kimanin matasa miliyan 35 ke fama da rashin aikin yi ko kuma rashin isasshen aiki.
Obi ya kuma yi zargin cewa fiye da ’yan Najeriya miliyan 40 na iya fuskantar matsananciyar yunwa zuwa ƙarshen 2026, tare da ci gaba da matsalolin ta’addanci, ’yan bindiga da satar mutane.
Ya ce abin da suka gani a sansanin ’yan gudun hijira na Ramin Kura da ke kusa da birnin Sokoto ya nuna irin wahalhalun da dubban mata da yara ke fuskanta sakamakon rashin tsaro.
Obi ya ce idan aka ba shi shugabanci, zai mayar da hankali wajen samar da tattalin arziki mai dogaro da noma, masana’antu da bunƙasa ɗan Adam, tare da yaƙi da ta’addanci da ’yan bindiga domin manoma su koma gonakinsu.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su riƙa neman shugabanni su ɗauki alhakin ayyukansu, yana mai cewa sauyin da ƙasar ke buƙata ba zai samu ta hanyar addu’a ko alkawura kaɗai ba.
