Rahotanni sun nuna cewa jihohi tara a Najeriya sun kashe makudan kudade fiye da adadin kudaden da suka samu a zangon farko na shekarar 2026, inda Jihar Akwa Ibom ta kasance kan gaba da gibin sama da naira biliyan 38.
Bayanan da NGF da TheCable Index suka wallafa sun nuna cewa Akwa Ibom ta kashe naira biliyan 201 da miliyan 730, yayin da kudaden shigarta suka tsaya kan naira biliyan 163 da miliyan 260.
Hakan ya haifar da gibin kasafin kudi na kimanin naira biliyan 38 da miliyan 470.
Jihar Kano ce ta biyu, inda ta kashe naira biliyan 159 da miliyan 890, amma ta samu kudaden shiga na naira biliyan 141 da miliyan 200, wanda ya bar gibin naira biliyan 18 da miliyan 690.
A jihar Bauchi kuwa, an kashe naira biliyan 144 da miliyan 450, yayin da kudaden shiga suka kai naira biliyan 127 da miliyan 200, lamarin da ya haifar da gibin naira biliyan 17 da miliyan 250.
Jihar Kogi ta kashe naira biliyan 89 da miliyan 850, sannan ta samu kudaden shiga na naira biliyan 79 da miliyan 30, da gibin naira biliyan 10 da miliyan 820.
Sauran jihohin da suka kashe fiye da kudaden shigarsu sun hada da Adamawa, wadda ke da gibin naira biliyan 6 da miliyan 920; Niger da gibin naira biliyan 5 da miliyan 250; da Jigawa wadda gibinta ya kai naira biliyan 3 da miliyan 820.
Haka kuma, jihar Ekiti ta samu gibin naira miliyan 590, yayin da Kaduna ta samu gibin kusan naira miliyan 180.
Wannan na nufin cewa a cikin watanni ukun farko na shekarar 2026, wadannan jihohi tara sun fuskanci yanayin da kashe-kashensu ya zarce kudaden shigarsu, wanda ke nuna bukatar karin hanyoyin samar da kudaden shiga ko kuma daidaita kashe-kashe domin rage gibin kudi.
