Farashin man fetur, wato PMS, na neman kai wa Naira 1,500 kan kowace lita, bayan da farashin ya tashi daga Naira 1,205 zuwa Naira 1,310 a jiya.
Wannan karin farashin ya zo ne duk da cewa farashin danyen mai a kasuwar duniya ya samu raguwar farashi, inda ya sauka daga dala 92 zuwa dala 87 da centi 31 kan kowace ganga.
Binciken jaridar Sunday Vanguard ya nuna cewa kamfanin MRS, wanda ke cikin manyan masu sayar da man fetur a Najeriya, ya kara farashin litar man fetur zuwa Naira 1,310, daga Naira 1,205 a Legas da kewaye.
Wannan sabon karin farashin na kara nuna yiwuwar cewa farashin litar man fetur zai iya kaiwa Naira 1,500 a wasu wurare idan aka ci gaba da samun karin farashi.
