Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta yi watsi da wani rahoto daga mujallar The Economist da ya nuna cewa akwai karuwar rashin jin daɗin ’yan Najeriya kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa har yanzu yana da damar lashe zaɓen 2027.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana rahoton a matsayin abin da ke ɗauke da “son zuciya” da kuma “zargi marar tushe”.
A cewar Dare, mujallar ta mayar da hankali ne kan matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta ba tare da la’akari da irin halin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta gada ba.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu tsauri tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023, ciki har da cire tallafin man fetur da sauye-sauyen tsarin canjin kuɗaɗen waje.
Fadar Shugaban Ƙasar ta kuma kare manufofin gwamnatin kan ilimi, albashi, tallafin manoma da kuma ’yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
A cewar gwamnatin, cire tallafin man fetur da sauran sauye-sauyen tattalin arziki sun haifar da matsin rayuwa a farkon lokaci, amma ana ganin su a matsayin matakan da za su taimaka wajen gyara tattalin arzikin ƙasar a dogon lokaci.
