Malaman Addini Sama da 1,000 Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Neman Wa’adi Na Biyu
ABUJA: Kimanin malaman addinin Musulunci 1,000 daga arewacin Najeriya sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye aniyarsa ta sake neman takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Malaman sun bayyana hakan ne a wani taron kasa da aka gudanar a Kano, inda suka tattauna halin da Najeriya ke ciki da kuma makomar zaben 2027.
A cikin sanarwar da suka fitar bayan taron, malaman sun bayyana damuwarsu kan matsalar tsaro, musamman kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke ci gaba da faruwa a wasu sassan kasar.
Sun kuma soki wasu daga cikin manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin canjin kudin Naira da karin kudin wutar lantarki da kuma wasu sauye-sauyen haraji.
Malaman sun ce idan gwamnati ba ta dauki matakan magance matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki ba, ya kamata ‘yan Najeriya su yi la’akari da zabar wani sabon shugabanci a 2027.
Sun kuma bukaci malamai da su rika fadin gaskiya ga gwamnati tare da gujewa zama kayan siyasa
