Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki shirin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen mai na NNPC, yana mai bayyana shi a matsayin matakin siyasa na wucin gadi da ba zai magance matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta ba.
Atiku, ta bakin daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya ce rangwamen bai kamata a ɗauke shi a matsayin mafita ga tsadar rayuwa ba, musamman ganin cewa bayan kwanaki 30 farashin zai koma yadda yake.
Ya ce gwamnati ba ta bayyana adadin kuɗin da za a rage wa mai mota kan kowace lita ba, sannan ba ta tabbatar da cewa rage farashin zai haifar da saukar kuɗin sufuri ga fasinjoji ba.
Atiku ya bayyana cewa abin da ake buƙata shi ne mafita mai ɗorewa, ba rangwame na ɗan lokaci ba. Ya kuma sake jaddada shawarar da ya gabatar ta samar da tallafin samar da man fetur da aka tace a cikin Najeriya, tare da tsara shi cikin kasafin kuɗi domin amfanin masu amfani da man da kuma bunƙasa matatun mai na cikin gida.
Ya ce: “Yan Najeriya na buƙatar sauƙi mai ɗorewa, ba ƙirga kwanakin da wahala za ta dawo ba.”
Atiku ya kuma bayyana cewa idan ya samu damar jagorantar ƙasar, zai mayar da hankali wajen rage tsadar rayuwa, yana mai cewa: “Tinubu ya sa rayuwa ta yi tsada; ni kuma zan sa rayuwa ta zama mai sauƙi.”
