Gwamnatin Tarayya ta ce tana da shirin yi wa ’yan Najeriya 25,000 tiyatar cire yanar idon kyauta kafin ƙarshen shekarar 2027, domin rage makanta da za a iya kauce wa ta hanyar samun magani.
Ministan Lafiya, Iziaq Salako, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Kula da Lafiyar Ido ta Duniya ta shekarar 2026 a Abuja.
Ya ce shirin zai gudana ne ƙarƙashin shirin Renewed Hope Health Connect Initiative, wanda ke da nufin kusantar da ingantaccen kulawar ido ga ’yan Najeriya.
Ministan, wanda daraktar sashen kiwon lafiya ta yanar gizo, Doris Aneke, ta wakilta, ya bayyana cewa cutar ido na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa makantar da za a iya magancewa.
Ya ce gwamnati ta horar da ma’aikatan lafiya sama da 3,000 a jihohi 16, tare da samar da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko sama da 1,400 domin kula da ido.
Haka kuma, ya bayyana cewa an raba tabarau sama da miliyan 1.5 ga al’umma a jihohi 16, yayin da aka duba lafiyar idanun yara sama da miliyan 1.5 masu zuwa makaranta.
Salako ya ƙara da cewa gwamnati na shirin faɗaɗa shirin raba tabarau zuwa wasu jihohi 10, tare da kafa sabbin cibiyoyin kula da gani guda huɗu a asibitocin jihohin Enugu, Edo, Sokoto da Nasarawa.
