Sabon rikici ya kunno kai a Jihar Yobe bayan rahotannin kama fitaccen ɗan siyasa, Wakil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, bisa zargin taimaka wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da kayayyaki da sauran buƙatu.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa sojojin Operation HADIN KAI ne suka kama ɗan siyasar a ranar Asabar, bayan wani binciken sirri da ya danganta shi da mutanen da ake zargin suna taimaka wa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
ZARGIN SHIGA TSAKANIN SOJOJI DA WAƊANDA AKA KAMA
A cewar wasu majiyoyi masu masaniya kan aikin soji, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu, kamen Mai Salati ya biyo bayan zargin yunƙurinsa na ba jami’an soji kuɗi domin a saki wasu mutanen da aka kama a Kanamma, Jihar Yobe.
Majiyoyin sun ce kwamandan Sector 2 da rundunar 27 Task Force Brigade sun gudanar da binciken sirri kafin a kama ɗan siyasar, wanda ake zargin yana da hannu wajen samar da kayayyaki da sauran buƙatu ga ’yan Boko Haram da ISWAP.
Rahoton ya ƙara da cewa, lokacin da ake shirin miƙa mutanen da aka kama domin ci gaba da bincike, Mai Salati ya yi yunƙurin shiga tsakani domin a sake su ta hanyar bayar da kuɗi ga jami’an soji.
Sai dai, a cewar majiyoyin, jami’an sun ƙi karɓar kuɗin, suka kama shi tare da fara shirye-shiryen miƙa shi Maiduguri domin zurfafa bincike da yiwuwar ɗaukar matakin shari’a.
Haka kuma, Daily Nigerian ta ce ta ga wani faifan bidiyo da ake zargin yana nuna ɗan siyasar yana ƙoƙarin miƙa kuɗi ga jami’an soji dangane da batun sakin waɗanda aka kama.
ANA ZARGIN BATUN NA DA ALAƘA DA SIYASA
Kamen ya haifar da muhawara a tsakanin al’umma, inda wasu ke nuna damuwa kan yiwuwar akwai siyasa a cikin lamarin.
Sai dai, har yanzu zargin da ake yi wa Mai Salati na buƙatar cikakken bincike, kuma ba a gabatar da hukuncin kotu da ya tabbatar da laifin ba.
ƘUNGIYA TA YI KIRA DA A BAR HUKUMOMI SU YI AIKI
A wani ɓangare na lamarin, ƙungiyar Yobe Network Against Violent Extremism ta yi kira ga al’umma da ’yan siyasa da su bai wa hukumomin tsaro damar kammala bincikensu ba tare da katsalandan ba.
A cikin sanarwar da jagoran ƙungiyar, Ibrahim Goni, ya fitar, ya yi gargaɗin cewa yaɗa jita-jita a kafafen sada zumunta ko mayar da batun rikicin siyasa na iya karkatar da hankalin hukumomin tsaro daga aikinsu.
Ibrahim Goni ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas ya sha fama da matsalar ta’addanci, wadda ta haddasa asarar rayuka, raba iyalai da dama da muhallansu, tare da jefa al’umma cikin mawuyacin hali.
Ya jaddada cewa duk wani sahihin zargi da ya shafi ba ’yan ta’adda kuɗi, kayayyaki, ɗaukar ma’aikata, ɓoye su ko taimaka musu ta kowace hanya, ya kamata a bincika shi sosai ba tare da la’akari da matsayin siyasa ko zamantakewar wanda ake zargi ba.
Tambaya: Shin ya kamata a bar hukumomin tsaro su kammala binciken wannan lamari ba tare da tsoma bakin siyasa ba, ko kuwa akwai buƙatar a bayyana ƙarin bayanai domin kawar da shakku a tsakanin al’umma?
