Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya sunan tsohon Ministan Ƙirƙire-Ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Geoffrey Nnaji, cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar Enugu a zaɓen 2027.
Nnaji, wanda ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon zargin yin takardun shaidar karatu na bogi, shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, kuma sunansa ya bayyana a matsayi na 13 a cikin jerin da INEC ta fitar a daren Asabar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a cikin takardun da ya miƙa wa INEC, Nnaji ya gabatar da sakamakon jarrabawar WAEC, ba tare da haɗa takardar shaidar digirin jami’a da ake takaddama a kai ba.
A shekarar 2023, wani bincike da jaridar Premium Times ta gudanar ya yi zargin cewa Nnaji ya miƙa takardun shaidar karatu da na yi wa ƙasa hidima (NYSC) na bogi ga Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa lokacin tantance shi domin naɗa shi minista.
Rahoton ya kuma yi zargin cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta musanta bayar da takardar shaidar digirin da aka danganta da Nnaji, tana mai cewa an shigar da shi jami’ar a shekarar 1981, amma bai kammala karatunsa ba.
Binciken ya ƙara bayyana cewa Nnaji ya amince a cikin takardar rantsuwa da aka gabatar a kotu cewa jami’ar ba ta ba shi takardar shaidar digiri ba, kuma bai taɓa karɓar irin wannan takarda ba.
Haka kuma, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuffuka masu Alaƙa da Ita (ICPC) ta kama Nnaji a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar 1 ga Yuli, 2026, bayan da ta ce ya yi biris da gayyatar da ta aika masa.
Daga bisani, an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zarge-zargen ƙirƙirar takardun shaida na bogi, amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba da kuma halatta kuɗaɗen haram.
Nnaji ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su, kuma kotu ta bayar da belinsa kan kuɗi Naira miliyan 20 tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa.
A halin yanzu, sunansa na cikin jerin ’yan takarar gwamnan Enugu da INEC ta fitar domin zaɓen 2027.
