Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta rika ba wa gidajen da suka fi fuskantar matsin tattalin arziki a kasar tallafin kuɗi kai tsaye.
IMF ya yi wannan kiran ne yayin da yake fitar da rahotonsa na hasashen tattalin arzikin duniya na watan Oktoba 2026 (WEO), a yayin taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya da ke gudana a Bangkok.
A cewar rahoton, IMF ya bayyana cewa bayar da tallafin kuɗi kai tsaye zai taimaka wajen rage talauci da inganta wadatar abinci, duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a ƙasar.
