Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 20, ciki har da jami’an tsaro, bayan sun kai hari kan ayarin ’yan kasuwa da ke tafiya ƙarƙashin rakiyar sojoji a Jihar Zamfara.
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar ya ce ’yan kasuwar na kan hanyarsu daga garin Gwashi zuwa kasuwar Nasarawa da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a ranar Asabar, lokacin da maharan suka yi musu kwanton ɓauna da misalin ƙarfe 2 na rana.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai sojoji huɗu, ’yan sanda uku, jami’in Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) guda ɗaya da fararen hula 12.
Wata majiya daga rundunar soji ta kuma bayyana cewa mutane 19 sun jikkata sakamakon harin.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun hare-haren ’yan bindiga a sassa daban-daban na Jihar Zamfara.
A watan da ya gabata, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da malaman addinin Musulunci shida a kan hanyar Dakko zuwa Damri, a ƙaramar hukumar Bakura ta jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya ce malaman na kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara ne lokacin da maharan suka tare motarsu tare da yin garkuwa da su.
Haka kuma, a watan Yuni, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai bakwai na Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda, bayan sun kai hari gidansu a yankin Low-Cost na garin.
’Yansandan sun bayyana a lokacin cewa jami’an tsaro, tare da sojojin Operation Fansan Yamma, sun fara bin sawun waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban domin ceto su.
