IMF ya gargaɗi Najeriya kan dawo da tallafin man fetur
Asusun ba da lamuni na Duniya (IMF) ya gargaɗi gwamnatin Najeriya kan sake dawo da tallafin man fetur ga kowa da kowa, inda ya ba da shawarar tallafin kuɗi na musamman ga magidanta da ke fama da tsadar rayuwa.
Daraktan sashen kuɗaɗen gwamnati na IMF, Rodrigo Valdés, ne ya bayyana hakan yayin taron shekara-shekara na asusun da Bankin Duniya a Bangkok, Thailand, ranar Laraba.
Valdés ya ce dawo da tallafin man fetur na bai ɗaya zai jefa gwamnati cikin ƙarin kashe kuɗi, tare da fifita masu kuɗi waɗanda suka fi amfani da man fetur fiye da talakawa.
Ya ce kare al’umma daga tsadar rayuwa ba yana nufin dole ne gwamnati ta hana farashin man fetur tashi ba, yana mai cewa akwai hanyoyin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi ba tare da dawo da tallafin ga kowa ba.
IMF ta ba da shawarar tallafa wa fasinjojin motocin haya, rage kuɗin sufuri, bayar da tallafin kuɗi kai tsaye ga magidanta da suka cancanta, da kuma ƙarfafa shirye-shiryen ciyar da ɗalibai a makarantu.
Wani jami’in asusun, Davide Furceri, ya ce gwamnati za ta iya amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen da take kashewa wajen tallafin man fetur domin rage kuɗin mota ga jama’a da kuma taimaka wa manoma masu ƙaramin ƙarfi.
Asusun ya kuma bayyana cewa duk da ci gaban da Najeriya ta samu wajen daidaita tattalin arziƙi bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023, har yanzu talakawa da dama na fuskantar matsin tattalin arziƙi.
Rahoton IMF ya nuna cewa kashi 63 cikin 100 na ’yan Najeriya na rayuwa cikin talauci bisa ma’aunin talaucin ƙasar, yayin da mutane miliyan 27 suka fuskanci matsalar ƙarancin abinci a kaka ta shekarar 2025.
Haka kuma, asusun ya bayyana cewa magidanta miliyan 9.2 ne aka yi wa rajista a shirin tallafin kuɗi na kai tsaye da aka samar tare da goyon bayan Bankin Duniya, duk da cewa burin shirin shi ne ya kai ga magidanta miliyan 15.
IMF ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta faɗaɗa bayar da tallafin kuɗi ga masu buƙata, tare da tabbatar da cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur wajen rage radadin tsadar rayuwa.
Asusun ya jaddada cewa tallafin da ake bayarwa ya kamata ya kasance na ɗan lokaci, wanda aka ware wa waɗanda suka fi buƙata, domin kare talakawa ba tare da ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati ba.
