Ba za mu yi ‘bushasha’ a bikin samun ’yancin kan Nijeriya karo 66 ba- Gwamnatin Tinubu
Gwamnatin Nijeriya ta ce ta shirya gudanar da bikin cikar kasar shekaru 66 da samun ’yancin kai cikin yanayin daidai ruwa daidai tsaki, inda shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi ga ’yan ƙasa a ranar 1 ga Oktoba.
Jaridar Punch ta ruwaito ofishin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya bayyana cewa an kafa kwamitin ministoci da manyan jami’an gwamnati da zai jagoranci shirye-shiryen bikin a Abuja, tare da Akume a matsayin shugaban kwamitin.
