Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana cewa shari’ar da ake yi a gaban Kotun Tarayya ta Amurka da ke Washington, D.C., ba shari’ar laifi ba ce a kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, illa takaddama ce kan bukatar bayyana wasu bayanan hukumomin Amurka karkashin dokar Freedom of Information Act (FOIA).
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis, fadar ta ce FBI da DEA sun riga sun gabatar da shafuka 399 na bayanai amma sun boye wasu bangarori bisa tanade-tanaden doka, inda yanzu babbar takaddamar da ta rage ita ce ko boye wadannan bayanai ya dace da dokar Amurka.
Sanarwar ta jaddada cewa fitar da bayanan ko kin fitar da su ba ya tabbatar da aikata wani laifi, tana mai kira ga kafafen yada labarai da jama’a su bambance tsakanin sahihin tsarin shari’a da rade-radin siyasa.
