Ƙungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta ce gidajen mai a Abuja da kewaye za su fara rage farashin man fetur a cikin kwanaki masu zuwa, da zarar sabbin kayayyakin mai sun fara shigowa kasuwa.
Sakataren yaɗa labarai na kasa na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Alhamis.
Ukadike ya ce dillalan man na shirin sauya farashi da dabarun sayar da man domin dacewa da sabon yanayin kasuwa, duk da cewa har yanzu ba a kayyade takamaiman lokacin shigowar sabbin kayayyakin ba.
Ya ce da zarar an fara sayen sabbin kayayyakin, dillalai za su gaggauta duba farashinsu tare da fara samar da man ga masu amfani.
Rahoton NAN ya ce matakin ƙara farashin man da matatar Dangote ke sayarwa daga N1,165 zuwa N1,185, N1,200 sannan N1,265 kan lita a cikin makon da ya gabata ya jawo tashin farashin man a gidajen mai na Abuja.
Wasu masu ababen hawa sun nuna damuwa kan tsadar man, inda suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan da za su daidaita farashin man fetur.
