Hukumar zabe ta ƙasa (INEC) na shirin bayyana matsayinta kan halaccin wasu ‘yan takara a zaben 2027, biyo bayan hukuncin Kotun Koli kan dokokin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zai yi taron manema labarai a yau, Talata, inda ake sa ran zai bayyana matsayin hukumar da kuma makomar ‘yan takarar da hukuncin Kotun Koli ya shafa.
Kotun Koli ta tabbatar da ingancin sashe na 77 da 84 na Dokar Zabe ta 2026, wadanda suka tanadi cewa jam’iyyu su mika wa INEC rajistar mambobinsu kafin zaben fidda gwani, kuma wadanda ba sa cikin rajistar ba ba su da damar kada kuri’a ko neman takara.
A Gombe, ana nuna damuwa kan makomar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, wanda ya bar APC ya koma PDP bayan ya janye daga takarar gwamnan Gombe a karkashin APC.
Sai dai wasu jagororin PDP sun ce hukuncin Kotun Koli bai tabbatar da cewa Pantami ba ya cikin rajistar PDP ba, yayin da aka kuma gudanar da sabon zaben fidda gwani a jam’iyyar bayan kotu ta soke na farko.
A Jihar Neja kuma, ana tambayar halaccin takarar Muhammad Nami na PDP, bayan zargin cewa ya kasance dan takarar sanata na APC kafin daga bisani ya zama dan takarar gwamnan PDP.
Wani lauya mai kula da kundin tsarin mulki, Abdulmumin Jibril Abdullahi, ya ce hakan na iya jefa takarar Nami cikin kalubalen shari’a idan aka tabbatar da cewa ba a saka sunansa cikin rajistar mambobin PDP da aka mika wa INEC cikin wa’adin da doka ta tanada ba.
Haka kuma, hukuncin ya haifar da ce-ce-ku-ce kan takarar tsohon Sufeto-Janar na ’yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, a Nasarawa, wanda ya maye gurbin dan takarar SDP bayan ya janye daga takarar.
Sai dai magoya bayan tsohon IGP sun ce tsarin da ya kai shi takara ya bi doka, tare da jaddada cewa ba shi ne wanda ya shigar da karar da Kotun Koli ta yanke hukunci a kai ba.
Sashe na 77 na Dokar Zabe ta 2026 ya bukaci jam’iyyu su mika rajistar mambobinsu ga INEC akalla kwanaki 21 kafin zaben fidda gwani, tare da hana amfani da wata rajista daban wajen gudanar da zaben fidda gwani.
Daily Trust Hausa
