Hukumar EFCC ta ce ta kwato sama da Naira tiriliyan 1.23 cikin watanni 34 na shugabancin Ola Olukoyede, adadin da ta ce shi ne mafi girma a tarihin kwato kudade na hukumar.
Shugaban EFCC Ola Olukoyede, ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da rahoton ayyukansa a Abuja.
Ya ce hukumar ta karɓi koke-koke 49,673, ta gudanar da bincike kan 39,615, sannan ta gurfanar da mutane a gaban kotu a shari’o’i 14,476, inda aka samu hukunci 10,872.
Olukoyede ya kuma ce EFCC ta kwato kadarori sama da 10,000, ciki har da gidaje, motoci, filaye da sauran kadarori, tare da mayar da daruruwan biliyoyin naira ga gwamnati da sauran wadanda abin ya shafa.
Ya ce nasarorin sun hada da karfafa yaki da cin hanci, damfara ta yanar gizo, safarar kudade da sauran laifukan tattalin arziki.
