Kungiyoyin ma’aikatan lafiya a jihar Katsina sun sanar da cewa za su fara yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki bakwai daga ranar 8 ga Satumba, 2026, saboda gazawar gwamnatin jihar wajen magance wasu buƙatunsu da suka daɗe suna gabatarwa.
Jaridar Premium Times, ta rawaito cewa ƙungiyar Assembly of Health Care Professionals ta Katsina ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a birnin Katsina.
