Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ci gaba da fasakwaurin man fetur zuwa ƙasashen maƙwabta na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa farashin man yake da tsada a Nijeriya.
Dangote ya bayyana cewa farashin man fetur a ƙasashen maƙwabta ya zarce na Nijeriya da kashi 30 zuwa 50 cikin ɗari, yana mai cewa wannan bambancin farashi yana ƙara bai wa masu fatauci da ’yan fasakwauri kwarin gwiwa wajen fitar da man daga Nijeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a ranar Talata, yayin da yake magana kan farashin fetur da kuma samuwar man a kasuwa a daidai lokacin da ake fama da rikicin Gabas ta Tsakiya.
Dangote ya ce ba za a iya kallon farashin fetur a Nijeriya shi kaɗai ba tare da la’akari da farashin man a ƙasashen da ke makwabtaka da Nijeriya ba.
Ya ce idan aka kwatanta farashin fetur a Nijeriya da na ƙasashen da ke kusa da ita, za a ga cewa akwai babban bambanci, wanda ke ƙarfafa masu safarar man su fitar da shi daga ƙasar.
Ɗangote ya ce har yanzu ana samun yawan fasakwaurin man fetur da ake samarwa a Nijeriya zuwa ƙasashen maƙwabta.
Ɗangote ya ce har yanzu ana samun yawan fasakwaurin man fetur da ake samarwa a Nijeriya zuwa ƙasashen maƙwabta.
A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ke safarar man na iya sayen fetur a Nijeriya sannan su fitar da shi zuwa wata ƙasa, inda za su samu ƙarin kuɗi saboda bambancin farashin man.
Dangote ya bayyana cewa farashin fetur a wasu ƙasashen maƙwabta ya fi na Nijeriya da kashi 30 zuwa 50 cikin ɗari.
Ya ce wannan babban bambancin farashi yana sa safarar fetur zuwa ƙasashen maƙwabta ta zama wata hanya da masu fasakwaurin ke ganin za su iya samun riba cikin gaggawa.
Dangote ya bayar da misalin Jamhuriyar Nijar, inda ya ce farashin fetur ya fi na Nijeriya da kusan kashi 20 zuwa 25 cikin ɗari.
Ya ce idan farashin fetur a Nijeriya ya kai Naira 1,350, farashin man a Nijar zai iya kasancewa sama da haka da kashi 20 zuwa 25 cikin ɗari.
