Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi bayani kan yadda ake tafiyar da kudaden da Najeriya ke samu daga man fetur, da kuma kudaden da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, yayin da farashin man fetur ya tashi zuwa Naira 1,450 kan kowace lita.
Sabbin karin farashin man fetur sun biyo bayan karuwar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya haifar da tashin farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya.
Bincike ya nuna cewa wasu gidajen mai da dama a Abuja, babban birnin tarayya, sun kara farashin man fetur zuwa tsakanin Naira 1,395 da Naira 1,450 kan kowace lita.
A cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Litinin, Atiku ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gaza yin cikakken bayani kan kudaden da kasar ke samu, cire-ciren da ake yi daga asusun tarayya, da sauran mu’amalolin da suka shafi man fetur.
Atiku ya ce an sha gaya wa ‘yan Najeriya cewa cire tallafin man fetur zai samar da karin kudaden da za a zuba wajen ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da sauran muhimman ayyuka na kasa.
