Shugaban darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yana shirye ya sasanta da Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf.
Yusuf, wanda yake ɗaya daga cikin jiga-jigan masu biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya, ya lashe zaɓen gwamna a shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa APC.
Wannan sauyi ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin Kwankwaso da Yusuf, wanda ya yi wa Kwankwaso aiki a matsayin mataimaki tsawon kusan shekaru 40.
Sai dai a wata hira da ya yi da BBC Hausa, wadda aka wallafa a shafinsa na sada zumunta da aka tantance, Kwankwaso ya ce a shirye yake ya yafe wa Yusuf kuma su sasanta, idan Yusuf shi ma yana son hakan.
Kwankwaso ya ce bai yi watsi da Yusuf ba, kuma bai nemi Yusuf ya sauya jam’iyyar siyasa ba.
