Rikicin siyasa tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wasu gwamnonin jam’iyyar APC ya sake daukar sabon salo yayin da ake kara kusantar babban zaben shekarar 2027.
Tushen rikicin shi ne wata kungiyar siyasa mai suna “Rainbow Coalition”, wadda Wike ke jagoranta domin tattara goyon baya ga sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Wike ya bayyana cewa manufar kungiyar ita ce hada ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban domin su mara wa Tinubu baya a zaben shugaban kasa, ba tare da tilasta musu barin jam’iyyunsu baSai dai gwamnonin APC, karkashin kungiyar Progressive Governors’ Forum, sun nuna damuwa cewa irin wannan tsari na iya raba kuri’un APC a zaben gwamna, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da kuma majalisun jihohi.
Matsayinsu shi ne cewa ‘yan APC su goyi bayan dukkan ‘yan takarar APC a kowane mataki, ba wai shugaban kasa kadai ba.A taron gwamnonin APC da aka yi ranar 14 ga Satumba, shugaban kungiyar kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce gwamnonin ba za su amince da wata hadaka ko tsari da zai iya raunana APC ko ya jefa jam’iyyar cikin rudani ba.
Gwamnonin sun ce suna son yakin neman zaben 2027 ya kasance karkashin tutar APC, tare da cikakken goyon baya ga ‘yan takararta daga shugaban kasa zuwa mukaman jihohi da na majalisa.
