Kafafen sada zumunta sun cika da martani bayan an ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, tsohon Sanata Dino Melaye, ɗan kasuwa Ben Murray-Bruce da Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, tare a wani taron shagalin biki kafin aure a Marbella, Málaga, a ƙasar Spain.
Rahotanni sun bayyana cewa taron na daga cikin shirye-shiryen da ake gudanarwa gabanin bikin auren Saraya Danjuma da Bawa Salaka.
Wani bidiyo daga taron ya bazu sosai a kafofin sada zumunta ranar Asabar, inda aka ga wasu fitattun ƴan Najeriya daga cikin baƙin da suka halarci taron.
Rahotanni sun ce an gudanar da taron ne a La Cabane, wani wurin shakatawa mallakin Dolce & Gabbana da ke Málaga, inda wasu fitattun ƴan Najeriya suka halarta.
Kasancewar waɗannan fitattun mutane tare a wuri guda ya ja hankalin jama’a musamman saboda bambance-bambancen alaƙarsu da harkokin siyasa da kuma matsayinsu a idon jama’a.
Bidiyon da ke yawo a kafofin sada zumunta ya nuna ƙungiyar cikin annashuwa a Marbella, yayin da suke halartar wasu abubuwan da suka shafi shagulgulan bikin auren.
Taron ya haifar da ra’ayoyi mabanbanta, inda wasu masu amfani da kafofin sada zumunta suka yi tambaya kan yadda fitattun ƴan Najeriya suka taru a wajen ƙasar, duk da bambance-bambancen siyasa da kuma damuwar da ake da ita game da halin tattalin arzikin Najeriya.
Sai dai wasu sun bayyana cewa kasancewar waɗannan fitattun mutane a taron sirri guda ba ya tabbatar da cewa akwai wata ƙawancen siyasa, yarjejeniya ko wata haɗakar aiki a tsakaninsu.
