Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 da ta ɗauki matakan rage farashin fetur tare da fara sake duba mafi ƙarancin albashin ma’aikata
.Ƙungiyar ta bayyana hakan ne bayan wani taron shugabanninta da aka gudanar a Abuja, inda ta nuna damuwa kan hauhawar farashin kayayyaki, raguwar darajar kuɗin naira da kuma wahalhalun da ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya ke fuskanta.
NLC ta buƙaci gwamnati ta rage farashin fetur zuwa matakin da yake a lokacin da aka sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi a shekarar 2024.Haka kuma, ƙungiyar ta nemi a fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi kafin ƙarshen Oktoba, tare da ba ma’aikata rangwamen haraji da kuma tallafin albashi domin rage musu nauyin tsadar rayuwa.
A cewar ƙungiyar, albashin da ma’aikata ke karɓa a yanzu ya yi rauni sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi, lamarin da ke ƙara musu wahalar biyan kuɗin abinci, sufuri, haya, lafiya da karatun yara.Wa’adin da NLC ta bayar ya fara ne ranar 9 ga Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza cika buƙatunta cikin wa’adin, za ta iya ɗaukar wasu matakai kamar yadda shugabanninta za su yanke.
Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, ba a tabbatar da wata amsa daga Gwamnatin Tarayya da ke nuna cewa ta amince da dukkan buƙatun ƙungiyar ba.
