NDC Ta Kori Ɗan Takararta a Borno Kan Zargin Yi Wa Atiku Kamfen
Jam’iyyar NDC a Jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na Majalisar Dokokin Jihar, Mohammed Bunu, bisa zargin yi wa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, kamfen.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 25 ga Oktoba, 2026, jam’iyyar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan gano kayan kamfen da ke ɗauke da tambarin ADC, hoton Atiku da kuma sunan Bunu.
Mataimakin shugaban NDC na jihar, Umar Fema, ya ce an fara binciken ne daga shugabancin mazabar Hausari, kafin a miƙa batun ga shugabancin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Maiduguri Metropolitan Council domin zurfafa bincike.
A cewar wasiƙar, an gayyaci Bunu sau biyu, a ranakun 23 da 24 ga Oktoba, domin ya kare kansa kan zargin, amma bai halarci zaman binciken ba.
Bayan nazarin rahoton kwamitin binciken, shugabancin jam’iyyar ya amince da shawarar cire shi daga takara, tare da miƙa matakin ga shugabancin NDC na jihar.
Sai dai jam’iyyar ta bayyana cewa cire Bunu daga matsayin ɗan takara ya bambanta da dakatarwa ko korarsa daga cikakken zama ɗan jam’iyyar, wanda ke buƙatar bin ƙa’idojin kundin tsarin jam’iyyar.
