Atiku ya zargi Tinubu da ruɗin tunani kan ɗora wa ’yan adawa alhakin yunwa da wahalar tattalin arziki
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna abin da ya kira ruɗin tunani, bisa zargin ɗora wa ’yan adawa alhakin matsin tattalin arziki da yunwar da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Atiku ya bayyana cewa bai dace gwamnatin Tinubu ta riƙa ɗora wa ’yan adawa alhakin matsalolin da suka shafi rayuwar al’umma ba, maimakon mayar da hankali kan matakan da za su sauƙaƙa wa ’yan Najeriya halin ƙuncin da suke ciki.
Wannan batu na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan halin tattalin arzikin Najeriya da kuma yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da ƙasar gabanin zaɓen 2027.
