Kwamishinan Matasa da Bunƙasa Wasanni na Jihar Borno, Sainna Buba, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya yi barazanar cutar da masu adawa da jam’iyyar APC ko waɗanda suka ƙi goyon bayanta a zaɓe.
Kwamishinan ya yi wannan barazana ne a yayin wani taron ƙaddamar da yaƙin neman goyon baya da ƙungiyar Tinubu City Boy Movement ta shirya domin nuna goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma yiwuwar sake tsayawarsa takara a zaɓen 2027.
A yayin jawabin nasa, Sainna Buba ya yi amfani da kalaman barazana da suka shafi yanke yatsu, inda ya gargadi masu sukar gwamnati da ‘yan adawa kan abin da zai iya biyo bayan nuna adawa da su.
Ya ce duk wanda ya nuna musu yatsa, a shirye suke su yanke masa yatsun, sannan ya ƙara da cewa duk wanda ya sake nuna musu yatsa za su karya masa yatsarsa.
Kwamishinan ya kuma yi magana kan rabon moriyar gwamnati bisa la’akari da goyon bayan siyasa, inda ya bayyana cewa waɗanda ba sa goyon bayan gwamnati za su iya fuskantar wariya wajen samun wasu daga cikin abubuwan da gwamnati ke samarwa.
Kalaman na kwamishinan sun haifar da damuwa da ce-ce-ku-ce, musamman saboda matsayin da yake riƙe da shi a cikin gwamnatin Jihar Borno.
