Rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA ta ce dakarunta sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda da ke ƙarƙashin jagorancin fitaccen ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu Filani, a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an halaka kwamandojin biyu ne yayin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri a kusa da ƙauyen Kogo, ranar Litinin, 31 ga Agusta 2026.
Rundunar ta bayyana sunayen waɗanda aka halaka da Hamisu, wanda aka fi sani da Mamiyo, da Umar Bocho.
DCL Hausa
