Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce ta kori ma’aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata saboda hannusu a cin hanci da sauran laifukan kuɗi.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce fiye da mutum biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari’a a kotu, yayin da ake shirya gurfanar da wasu.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙaddamar da sabbin matakan tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin ma’aikatanta, yana mai cewa EFCC ba za ta iya yaƙar cin hanci yadda ya kamata ba idan nata jami’an suna aikata irin wannan laifi.
Haka kuma ya ce hukumar ta ƙwace sama da naira tiriliyan 1.23 da wasu manyan kuɗaɗen ƙasashen waje tsakanin Oktoban 2023 da Yunin 2026.
BBC HAUSA
