Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma tsohon Ministan Ma’adinan Ƙasa, Kayode Fayemi, ya bayyana alkawarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur a matsayin dabarar siyasa ta neman kuri’u, ba manufar tattalin arziki ba.
Fayemi ya kwatanta matakin na Atiku da tikitin Muslim-Muslim.da jam’iyyar APC ta yi amfani da shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin Prime Time na Arise Television ranar Litinin.
Fayemi ya ce alkawarin dawo da tallafin man fetur zai iya samun karɓuwa daga ’yan Najeriya da cire tallafin ya fi shafa, musamman masu ƙaramin ƙarfi da ke fama da tsadar rayuwa.
Sai dai ya sake jaddada cewa yana goyon bayan cire tallafin man fetur, yana mai cewa ya daɗe yana fafutukar ganin an cire shi tun lokacin da yake shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya.
A cewarsa, Shugaba Bola Tinubu ya gaji wani aiki da gwamnatin da ta gabata ta riga ta kammala a kan cire tallafin, amma ya ce matsalar da yake da ita ita ce yadda aka aiwatar da manufar.
Fayemi ya kuma ce tun kafin cire tallafin, gwamnonin jihohi sun yi aiki tare da gwamnatin tarayya da Bankin Duniya wajen samar da wani tsarin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, domin rage musu radadin tasirin cire tallafin.
Ya ce Atiku na amfani da wahalhalun tattalin arzikin da ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi ke fuskanta wajen samun goyon bayan jama’a ta hanyar alkawarin dawo da tallafin.
Fayemi ya ce yawancin ’yan Najeriya ba sa mayar da hankali kan muhawarar tattalin arziki da ake yi kan tallafin, illa dai suna son samun damar biyan bukatun yau da kullum, ciyar da iyalansu da kuma tura ’ya’yansu makaranta.
Ya kuma danganta talauci da rashin daidaito da matsalar tsaro, yana mai cewa matsin tattalin arziki na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen ci gaba da samun ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a Najeriya
