Rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro a Jihar Katsina ta ce ta kashe ’yan bindiga 18 a wani artabu da aka yi a ƙauyen Gidan Iyado, cikin mazabar Kakumi da ke ƙaramar hukumar Bakori.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Litinin, 21 ga Satumba, 2026, bayan da jami’an suka samu bayanan sirri cewa wata ƙungiyar ’yan bindiga na shirin kai hari tare da sace mazauna yankin domin neman kuɗin fansa, a cewar Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina.
A cewar rahoton, rundunar haɗin gwiwar ta ƙunshi mafarauta, dakarun Community Watch Corps, da jami’an sa-kai na yankin.
Jami’an sun yi wa ƙungiyar kwanton ɓauna, sannan aka yi musayar wuta tsakaninsu da ’yan bindigar, lamarin da gwamnatin jihar ta ce ya kai ga kashe mutum 18 daga cikin waɗanda ake zargi da aikata fashi da makami da satar mutane.
