Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin gaggawa na musamman domin dakile barkewar cutar Diphtheria da ta shafi yara a wasu sassan jihohin Katsina da Kano.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Jama’a, Muhammad Ali Pate, ya bayar da umarnin daukar matakan gaggawa domin karfafa sa ido kan cutar, cike gibin allurar rigakafi da kuma tabbatar da cewa wadanda suka kamu da cutar sun samu magani cikin lokaci.
Gwamnatin ta ce matakan na daga cikin kokarin dakile yaduwar cutar tare da kare yara daga karin kamuwa.
