Jihar Katsina ta jagoranci jerin jihohin Najeriya da suka kashe sama da naira biliyan ɗaya kan harkokin noma a cikin watanni ukun farko na shekarar 2026.
Bayanan da NGF da TheCable Index suka fitar sun nuna cewa gwamnatin Jihar Katsina ta kashe jimillar naira biliyan 12 da miliyan 10 kan harkokin noma a zangon farko na shekarar.
Wannan adadi ya sanya Katsina a matsayi na farko a cikin jihohi 21 da suka kashe sama da naira biliyan ɗaya a fannin noma a wannan lokaci.
Jihar Legas ce ta biyo bayan Katsina da kashe naira biliyan 7 da miliyan 620, yayin da Benue ta kashe biliyan 6 da miliyan 580.
Niger ta kashe biliyan 6 da miliyan 30, Oyo biliyan 5 da miliyan 390, sannan Kaduna ta kashe biliyan 5 da miliyan 290.
Sauran jihohin da suka kashe sama da naira biliyan ɗaya sun haɗa da Akwa Ibom, Edo, Gombe, Bauchi, Kebbi, Taraba, Borno, Bayelsa, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Sokoto, Ogun, Zamfara da Kano.
A ƙarshen jerin, Kano ta kashe kusan naira biliyan ɗaya kan harkokin noma a zangon farko na shekarar.
Rahoton ya nuna cewa Katsina ta yi tazarar sama da naira biliyan 4 da miliyan 390 tsakaninta da jihar da ke matsayi na biyu, Legas.
