Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da rajistar NDC a matsayin jam’iyyar siyasa a Nijeriya
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ke Lokoja wanda ya umarci INEC ta cire NDC daga rajistar jam’iyyun siyasa.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito hukuncin da mafi rinjaye na alkalai biyu cikin uku suka yanke, kotun ta tabbatar da amincewar INEC da rajistar NDC, tana mai cewa babbar kotun ta yi amfani da ikonta ba daidai ba lokacin da ta sake duba hukuncin da ita kanta ta yanke a ranar 10 ga Disamba 2025
DCL HAUSA
