Kwamitin Haɗin Gwiwa na ƙungiyoyin manyan ma’aikatan jami’o’i, wato Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU), Non-Academic Staff Union of Educational and Associated Institutions (NASU) da kuma National Association of Academic Technologists (NAAT), reshen Jami’ar Jihar Kaduna ta buƙaci a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta cimma da ma’aikatan jami’o’in gwamnati a shekarar 2026.
Kungiyar ta bayyana cewa ya kamata a fara aiwatar da yarjejeniyar ba tare da ƙarin jinkiri ba, domin tabbatar da an cika abubuwan da aka amince da su tsakanin gwamnatin tarayya da ma’aikatan jami’o’in.
