Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na shirin ƙarfafa shirye-shiryen zaɓen 2027, yayin da adadin masu rijistar kaɗa ƙuri’a ke gab da kaiwa miliyan 100.
Hukumar ta kuma bayyana shirin amfani da wani tsarin sa ido na zamani (real-time tracker) domin bibiyar muhimman abubuwan da suka shafi shirye-shiryen zaɓen a Najeriya.
Wannan na daga cikin matakan da INEC ke ɗauka domin tabbatar da ingantaccen tsari da kuma ƙara gaskiya a zaɓen 2027.
