Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin samar da tsarin wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin kilowatt 11 zuwa 15 a rufin kowane gida a Najeriya cikin watanni 11, idan aka zaɓe shi a 2027.
Adebayo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatinsa za ta kafa masana’antun kera na’urorin hasken rana a sassa daban-daban na ƙasar tare da horas da ’yan Najeriya wajen girkawa da kula da su.
Ya ce irin waɗannan cibiyoyin samar da wutar lantarki za su iya samar da kusan megawatt 32,000, tare da samar da guraben ayyukan yi.
Adebayo ya kuma yi alkawarin inganta harkar makamashi, da magance satar ɗanyen mai, tare da fifita tace man fetur a cikin gida.
Ya ce gwamnati za ta iya zuba jari a muhimman fannoni kamar wutar lantarki, ilimi, jiragen sama da masana’antu domin bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
