Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin wanda ya cancanci zama shugaban Najeriya.
Obi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da ofishin yakin neman zaben Makinde, inda ya bukaci ‘yan siyasa su mayar da hankali wajen gina Najeriya mai hadin kai da adalci, maimakon siyasar rikici da sabani.
Ya kuma ce duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2027 ta hanyar sahihin zabe mai inganci, ya kamata sauran ‘yan siyasa su mara masa baya domin ceto kasar daga matsalolin da take fuskanta.
