Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi kwalejojin horas da malamai (Colleges of Education) kan bayar da shirye-shiryen digiri marasa inganci ƙarƙashin manufar Dual Mandate.
Ministar Ilimi ta Ƙasa, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta bayyana cewa dole ne kwalejojin su kasance da ƙwararrun malamai, isassun kayan aikin koyarwa da tsarin tabbatar da ingancin karatu kafin su fara ko faɗaɗa shirye-shiryen digiri.
Ta bayyana hakan ne a wani taron ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda aka ƙaddamar da sabon tsarin karatun Dual Mandate da kuma shirin dabarun ci gaban Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (NCCE) na shekarar 2026 zuwa 2031.
Ministar ta jaddada cewa nasarar manufar ba za ta dogara da yawan kwalejojin da suka fara bayar da digiri ba, sai dai ingancin karatun da kuma ƙwarewar malaman da suke samarwa.
Manufar Dual Mandate tana bai wa kwalejojin ilimi da suka cika ƙa’idoji damar ci gaba da bayar da takardar shaidar NCE, tare da bayar da digiri na farko a fannin ilimi, bisa amincewar hukumomin da abin ya shafa.
A nata ɓangaren, babbar sakatariyar NCCE, Dakta Angela Ajala, ta ce manufar na buƙatar inganta tsarin gudanarwa, koyarwa da koyo, samar da kuɗaɗen gudanarwa da kuma yadda ake tantance ingancin ilimi.
Ta kuma yi gargaɗin cewa sabon tsarin karatun ba zai kawo sauyi ba idan babu ƙwararrun malamai, kayan aikin zamani, ingantaccen shugabanci da isassun kuɗaɗen gudanarwa.
