Kwastam ta kama magungunan da ba su da rajista da wasu kayayyaki na Naira miliyan 721.9 a Sakkwato da Zamfara
Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Sakkwato da Zamfara, ta kama magungunan da ba su da rajista da wasu kayayyakin da aka shigo da su ta barauniyar hanya, waɗanda jimillar kuɗin harajinsu ta kai Naira miliyan 721.96.
Mukaddashin Kwanturolan Kwastam na yankin, Mataimakin Kwanturol Haliru Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Sakkwato, ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026.
Abdullahi ya ce kama magungunan da ba a yi musu rajista ba na nuna irin barazanar da fasa ƙwauri ke haifarwa ga lafiyar al’umma da tsaron rayukan ’yan Najeriya.
Ya bayyana cewa magungunan da aka kama sun haɗa da fakiti 100 na Quinine, fakiti 500 na Amodiaquine, fakiti 140 na Paracetamol, fakiti 300 na magungunan mura, kwali ɗaya na allurar rage raɗaɗi, kwalaye biyu na ruwan maganin Dynewell, kwali ɗaya na allunan Dynewell da kuma kwali ɗaya na maganin mura na Clear Cold.
Ya yi gargaɗin cewa amfani da magungunan da ba su da rajista na iya jefa lafiyar jama’a cikin haɗari, yana mai cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hana yaɗuwar irin waɗannan magunguna.
A cewarsa, “Rundunar za ta ci gaba da ayyukan yaƙi da fasa ƙwauri domin dakile haramtacciyar cinikayya da kuma kare lafiyar ’yan Najeriya da tattalin arzikinsu.”
Abdullahi ya ƙara da cewa an gudanar da samamen ne duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihohin Sakkwato da Zamfara. Ya danganta nasarar aikin da ci gaba da sa ido da jami’an rundunar ke yi.
Sauran kayayyakin da aka kama tare da magungunan sun haɗa da buhunan manyan kaya 599 na tsofaffin tufafi, buhu bakwai na tsofaffin jakunkunan mata, kwalaye 43 na sigari da kwalaye bakwai na kofi mai suna Akouna.
Haka kuma, rundunar ta ƙwace wata tsohuwar motar dakon kaya kirar DAF mai lambar rajista JEG 199 XA, wadda aka yi amfani da ita wajen jigilar kayayyakin.
Ya ce an gudanar da ƙwacen kayayyakin ne bisa tanade-tanaden sashe na 245 da na 248 na Dokar Hukumar Kwastam ta Najeriya ta shekarar 2023, waɗanda suka bai wa hukumar ikon ƙwace kayayyakin da doka ta tanadi a kwace.
A ƙarshe, Abdullahi ya yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa hukumar sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da fasa ƙwauri.
Ya kuma jaddada aniyar rundunar na dakile fasa ƙwauri, sauƙaƙa halastacciyar cinikayya da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati.
Ya gode wa Kwanturolan-Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, da sauran hukumomin tsaro da kuma kafafen yaɗa labarai bisa goyon bayan da suke bai wa rundunar.
