An kama wata mata mai suna Bilkisu Sani, mazauniyar karamar hukumar Rogo a jihar Kano, bisa zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu, wanda ake cewa yana shirin auren mata ta biyu.
Wani mazaunin yankin, Auwal Kazagi Rogo, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 7 na yamma a unguwar Katsalle da ke garin Rogo.
Ya ce mazauna yankin sun yi gaggawar zuwa wurin bayan sun ji ihun matar Gausu, wacce ta yi ikirarin cewa an yanka mijinta.
“Da muka isa wurin, sai muka ga ba a yanka shi ba, sai dai an buga masa abu a kai. Ya fadi cikin jini har ya mutu. Har ma akwai alamar cizo a kunnensa,” in ji Kazagi.
Ya kara da cewa an sanar da ‘yan sanda nan take, kuma daga baya suka dauki gawar domin gudanar da bincike.
Kazagi ya kara da cewa ana zargin Gausu ya yi alkawarin aure da wata mata kwanan nan, tare da shirin aurenta a matsayin mata ta biyu.
Wannan mataki nasa ya haifar da takaddama akai-akai tsakaninsa da Bilkisu, wacce ake zargin ta yi alwashin hana auren. Dattawan yankin sun taba shiga tsakani don sulhunta su, amma takaddamar ta ci gaba.
Kazagi ya ce tuni ‘yan sanda suka kama Bilkisu a matsayin wacce ake zargi da aikata laifin, yayin da ake ci gaba da bincike.
A daya bangaren kuma, an binne gawar mijin a safiyar ranar Asabar a Rogo bisa koyarwar addinin Musulunci.
Ma’auratan sun shafe kusan shekaru bakwai da aure kuma suna da ‘ya’ya biyu, sannan ana cewa a halin yanzu Bilkisu tana dauke da juna biyu na marigayin mijin nata.
Majiyoyi a yankin sun ce Gausu ya nemi iyalan wacce zai aura su gaggauta ranar bikin da watanni biyu saboda yadda matarsa ke nuna rashin amincewa da auren.
