Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada cewa ba ya nadamar matakin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta ɗauka, yana mai cewa babu shirin komawa tsohon tsarin bayar da tallafin.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taro mai taken “Together till 2027: An Evening with Original City Boy”, wanda ƙungiyoyin City Boy Movement da Relax-Tinubu-Is-Fixing-Nigeria suka shirya domin ƙarfafa goyon baya ga sake zaɓensa a babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban ƙasar ya ce Nijeriya na dab da shiga mummunan yanayin durƙushewar tattalin arziki kafin ya ɗauki matakin cire tallafin man fetur, yana mai nuna cewa matakin na daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar.
Sai dai cire tallafin ya ci gaba da zama babban batu da ke jawo muhawara a ƙasar, musamman ganin yadda hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa suka kasance cikin ƙalubalen da ’yan Nijeriya ke fuskanta.
Haka kuma, Tinubu ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ke neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, bayan da ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027.
Yayin da gwamnatin Tinubu ke ganin cire tallafin a matsayin matakin da ya zama dole domin sauya fasalin tattalin arzikin ƙasar, masu suka na ci gaba da nuna damuwa kan tasirin matakin ga rayuwar talakawa.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, batun tallafin man fetur na iya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan da za su mamaye fafatawar siyasa tsakanin Tinubu da ’yan adawa.
