Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa bankunan kasuwanci a ƙasar sun rufe jimillar rassa da cibiyoyin hada-hadar kuɗi 476 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.
Alkaluman da ke cikin CBN 2025 Statistical Bulletin for the Financial Sector sun nuna cewa adadin rassan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗi ya ragu daga 5,410 a shekarar 2022 zuwa 4,934 a 2025, wanda ke nuna raguwar kashi 8.8 cikin 100 cikin shekaru uku.
Rahoton ya nuna cewa wannan sauyi ya rage yawan wuraren da bankuna ke gudanar da harkokinsu na zahiri a faɗin Najeriya.
